Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 7:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa'ad da Almasihu ya zo, zai yi mu'ujizai fiye da na mutumin nan?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 7:31
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a.


Mutane duk suka yi al'ajabi, suka ce, “Shin, ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?”


Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu'ujizai da manyan al'ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.


Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi.


Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.


To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.


domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.


Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya.


Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”


Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”


Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.


Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.


“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”


Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ