24 Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.”
24 Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”
Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni.
Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa.
Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.
Masu hikima kuma sun faɗi waɗannan abu. Kuskure ne alƙali ya yi son zuciya.
Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ƙi suke ga Ubangiji.
ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?
“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.
Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari'ar gaskiya.
Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a, Ku daina goyon bayan mugaye!
“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce ku yi shari'ar gaskiya, bari kowa ya nuna alheri da jinƙai ga ɗan'uwansa.
Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba?
Ku dubi abin da yake bayyane mana! in dai wani ya amince na Almasihu ne, to, ya ƙara tunawa, wato kamar yadda yake shi na Almasihu ne, mu ma haka muke.