20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?”
20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”
Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”
Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.”
Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada.
Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”
Bulus na cikin kawo hanzarinsa, sai Festas ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Bulus, kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”
Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”
Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”
Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”
Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi.