Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 7:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 7:16
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.


Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa.


Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.


“Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.


Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.


Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.


Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu.


Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.


“Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa.


Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,


Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ