Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 6:71 - Littafi Mai Tsarki

71 Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

71 (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 6:71
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti.


Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.


To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,


da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.


Sai Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan, ya je wurin manyan firistoci don ya bashe shi a gare su.


Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”


Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bāshe shi, ya ce,


Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.


Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa'ad da Yesu ya zo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ