Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 6:61 - Littafi Mai Tsarki

61 Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

61 Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 6:61
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.


Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”


Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ