55 Domin naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika.
55 Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi.
Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne.
In kuwa Ɗan ya 'yanta ku, za ku 'yantu, 'yantuwar gaske.
Sa'an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama.
Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.
mai hidima a Wuri Mafi Tsarki, da kuma masujada ta gaskiya, wadda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba.
Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!”
Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.
Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne, Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.
Duk wanda suke cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.
Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa.