Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 6:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 6:26
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al'amuran duniya.


Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.


Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.


da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.


Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai.


Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya.


Ba su yi masa biyayya ba, Ba su yi aminci game da alkawarin da suka yi da shi ba.


Sa'ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”


Amma fa akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Domin tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bāshe shi.


Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


Sai suka ce masa, “To, wace mu'ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi?


Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.


Da jama'a suka ga mu'ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya.!”


Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ