18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.
18 Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya, Yakan yi walƙiya domin hadura, Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.
Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi, Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.
Sa'an nan kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa mangara tasa, gama iska tana gāba da su.
Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.
Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.