Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 6:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 6:11
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.


Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.


Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.


Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.


Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa'an nan ya gutsuttsura ya fara ci.


Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”


“Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”


Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi kai, da kuma gurasa.


Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi a na waɗanda kuka kama yanzu.”


Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ