sai ga wani mutum da aka haifa gurgu, ana ɗauke da shi. Kowace rana kuwa akan ajiye shi a ƙofar Haikali, wadda ake kira Ƙawatacciyar Ƙofa, don ya roƙi sadaka ga masu shiga Haikali.
Don lokaci lokaci wani mala'ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.]