Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.”
Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”
Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka.
Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”
Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.”