31 In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce.
31 “In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce.
Bari waɗansu su yabe ka ko da baƙi ne, faufau kada ka yabi kanka.
Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku.
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.