27 Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne.
27 Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa'azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.
tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari'a, shari'a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”
Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan,
wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala'iku da manyan mala'iku da masu iko suna binsa.
Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa.
Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma, Ya rufe fagen fama da gawawwaki, Zai kori sarakunan duk duniya.
Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya” sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”
Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”
amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya.