Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 5:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 5:24
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”


Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba.


Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”


Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.


Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”


Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.


Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”


Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu,


Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.


Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.


Mu kam, mun sani mun riga mun tsere wa mutuwa, mun kai ga rai saboda muna ƙaunar 'yan'uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman mutuwa yake yi.


Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba da ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.


To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.


Ga Gurasa mai saukowa daga Sama, domin kowa yă ci, kada ya mutu.


Ni ne Gurasan rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”


Wannan shi ne Gurasan da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ