1 Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.
1 Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.
“Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi.
“Sau uku cikin shekara mazajenku duka za su hallara a gabana, ni Ubangiji Allah na Isra'ila.
Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.
Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,
Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa.
“Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.