Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”
To, da Ikkilisiya ta raka su, suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tubar al'ummai, sun kuwa ƙayatar da dukan 'yan'uwa ƙwarai.
Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”