Maganarka da na samu na ci. Maganarka kuwa ta zama abar murna a gare ni, Ta faranta mini zuciya. Gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Mai Runduna.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”
Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.