30 Sai suka fito daga garin suka nufo shi.
30 Sai suka fita daga garin suka nufa inda yake.
Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.
Suna fita majami'a ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa.
Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”
Saboda haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su koma na ƙarshe.”
Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai, Kamar kurciyoyi suna komowa gida.
To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al'ummai, su kam za su saurara.”
“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”
Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”
Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”