Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 4:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 4:14
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.


Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba. Ba za su sha zafin rana da na hamada ba, Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su. Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.


ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba, ba za su ƙara jin zafin rana ko ƙuna ba sam,


Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”


Wannan shi ne Gurasan da ya sauko daga Sama, ba irin wadda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Gurasan nan zai rayu har abada.”


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


Ya buga mana hatiminsa cewa mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatanmu, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.


Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.


Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.


Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.


Ku kuma kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa.


Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan! Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome ba!


Zan bi da ku kullayaumin, zan biya bukatarku da abubuwa masu kyau, in sa ƙasusuwanku su yi ƙarfi, ku zama kamar lambun da ake masa banruwa, za ku zama kamar maɓuɓɓugar ruwa da ba ta ƙonewa.


Mutanena sun yi zunubi iri biyu, Sun rabu da ni, ni da nake maɓuɓɓugar ruwan rai, Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa, hudaddu, Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.


Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”


Kowace halitta mai rai da take cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu.


“Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.


Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”


Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai?


Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa.


Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.


Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”


A ranar ƙarshe ta idin, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha.


domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”


Duk da haka maɓuɓɓuga, ko tafkin ruwa ba za su haramtu ba, amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ