7 Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’
7 Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’
Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”
Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.
Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.
Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.
kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkakan da suke a cikin haske.
In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama?
Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai? Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?
Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji murya tasa,
Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.
Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.”