Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.
Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.
Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari'ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka'idar zunubi nake bauta wa.