To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?
Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, Matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa Ya ɗauki rabon masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu.”
Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.
“Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa.