Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne domin kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku 'yan yara, ina rubuto muku ne domin kun san Uba.
Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”
Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.
Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”