10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi a na waɗanda kuka kama yanzu.”
10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”
“Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”
Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.
Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi kai, da kuma gurasa.
Sai Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba.
Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin.
Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?”