Kada ta ci kowane irin abu da aka yi da inabi, kada kuma ta sha ruwan inabi ko abin sa maye. Kada ta ci haramtaccen abu, amma ta kiyaye dukan abin da na umarce ta.”
Sa'ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir'auna kuka domin abinci, sai Fir'auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.”
Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa'an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.