Igiyar aure tana wuyan mace, muddin mijinta yana da rai. In kuwa mijinta ya mutu, to, tana da dama ta auri wanda take so, amma fa, sai mai bin Ubangiji.
Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.
bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.