“Sau uku a shekara dukan mazajenku za su zo, su hallara a gaban Ubangiji Allahnku a inda zai zaɓa, wato a lokacin idin abinci marar yisti, da lokacin idin makonni, da kuma a lokacin Idin Bukkoki. Kada su hallara a gaban Ubangiji hannu wofi.
Suka iso Urushalima. Ya shiga Haikalin ya fara korar masu saye da sayarwa daga ciki, ya kuma birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai,
Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.