8 Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata.
8 Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi,
Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata.
Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”
Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba.