A kan wannan Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.”
“Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”
Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”