Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 18:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 18:20
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu?


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


“Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni, Ku ji abin da nake faɗa. Tun da farko na yi magana da ku a fili, A koyaushe nakan cika maganata.” (Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)


Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.


Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.”


Ya yi ta koyarwa a majami'unsu, duk ana girmama shi.


Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.


Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


Ba a ɓoye na yi magana ba, Ban kuwa ɓoye nufina ba. Ban ce jama'ar Isra'ila Su neme ni a kowace hanyar ruɗami ba. Ni ne Ubangiji, gaskiya kuwa nake faɗa, Ina sanar da abin da yake daidai.”


Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi nake shaida wa duniya.”


Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.


Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba.


Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar.


Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!


Ai, al'amarin nan sananne ne ga sarki, ina kuma masa magana gabagaɗi ne, gama na tabbata ba abin da ya kuɓuce wa hankalinsa cikin al'amarin nan, don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba.


Saboda haka in sun ce da ku, ‘Ga shi can a jeji,’ kada ku fita. In kuwa sun ce, ‘Yana can cikin lolloki,’ kada ku yarda.


A taron dukan jama'arka, ya Ubangiji, Na ba da albishir na cetonka. Ka sani ba zan fasa hurta shi ba.


Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi, Zan yabe ka cikin taronsu.


Ya ko faɗi wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawatar masa.


Wannan kuwa a majami'a ya faɗa, sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.


Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ