7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka yake.
7 Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito.
Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”
Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu.
Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.
A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku.
“Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka.
Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.