zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.
Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin Allah ya yaɗu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, domin a ɗaukaka Allah.
In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.
To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?
Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima, Ba zan yi shiru ba, Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske, Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.
Don ko da na gaya masa cewa, ina 'yar taƙama da ku, ban kunyata ba. Kamar yadda duk abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka kuma taƙamarmu da ku a idon Titus ma ta zama gaskiya.
wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.