Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.
Ya ku 'yan'uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya.
Mu dukanmu kuma, fuskokinmu ba lulluɓi, muna nuna ɗaukakar Ubangiji, kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji kuwa wanda yake ruhu, yana zartar da haka.