9 Wato a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba,
9 a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba;
Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.
Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.
ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.
Dā kam, sa'ad da ban san shari'a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu.
Sa'ad da kuwa ya zo zai faɗakar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.