Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 16:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 16:5
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.”


Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa'an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.


Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”


Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi.


a kan adalci, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba.


muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.


Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama.


Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma,


“Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.”


Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.


Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā?


Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.


Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ