31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata?
31 Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata!
Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”
Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”
To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.