Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu!
Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.
Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?