Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 16:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Domin za ni wurin Uba’?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 16:17
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Bayan ɗan lokaci kaɗan, ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, za ku gan ni.”


Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’


Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambaya tasa.


Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?


Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?”


Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi.


Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.


Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna komece ce ma'anar tashi daga matattu.


“Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe.


Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?”


Amma ba su fahimci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.


Suka ce, “Me yake nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan’ ɗin? Ai, ba mu san abin da yake faɗa ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ