Don sa'ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagadin hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda kuke yi wa sujada ba a tare da kun san shi ba, shi nake sanar muku.
Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga 'yan'uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba'a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!
Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami'u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana.
Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.