13 Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa.
13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.
Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.
kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.
“Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi.
Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.
Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa.