Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.
Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunarku.” Amma ku kuka amsa kuka ce, “Ta yaya kake ƙaunarmu?” Ubangiji ya amsa, ya ce, “Ashe, Isuwa da Yakubu ba 'yan'uwan juna ba ne? Amma zuriyar Yakubu nake ƙauna.