Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 15:10 - Littafi Mai Tsarki

10 In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 15:10
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina.


Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne.


Amma duk wanda yake kiyaye maganarsa, wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa.


Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa'an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.


Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, domin koyaushe ina aikata abin da yake so.”


Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.


Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,


Na ɗaukaka ka a duniya da yake na cika aikin da ka ba ni in yi.


sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”


Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi.


Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, domin su sami izinin ɗiba daga itacen rai, su kuma shiga birnin ta ƙofa.


Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.”


Don kaciya da rashin kaciya ba sa hassala kome, sai dai kiyaye umarnin Allah.


Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai.


Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi.


Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa.


Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.


Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarninsa.


Kowa ya ce yana zaune a cikinsa, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.


Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.


Gama na kiyaye dokar Ubangiji, Ban yi wa Allahna tayarwa ba.


Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ