Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi kyau. Ta yaya ka lalace haka ka zama rassan kurangar inabi ta jeji, Waɗanda ba zan yarda da su ba?
Lokaci na zuwa sa'ad da Ubangiji zai sa kowane tsiro da kowane itacen da take a ƙasar su girma su yi kyau. Dukan jama'ar Isra'ila waɗanda suka ragu za su yi fāriya, su yi murna saboda amfanin da ƙasar take bayarwa.
Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa.
Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.
“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.
Isra'ila kurangar inabi ce mai bansha'awa Wadda yake ba da 'ya'ya da yawa. Ƙara yawan arzikinsu, Ƙara gina bagadansu. Ƙara yawan wadatar ƙasarsu. Ƙara kyautata ginshiƙansu.
Za mu tashi da sassafe, mu duba kurangun inabi, Mu ga ko sun fara tohowa, Ko furanni sun fara buɗewa. Mu ga ko itatuwan rumman sun yi fure. A can zan bayyana maka ƙaunata.
Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.
Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,