Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 14:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 14:11
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”


Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.


Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa.


“Ya ku 'yan'uwa, Isra'ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu'ujizai, da abubuwan al'ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani,


sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?”


A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ