24 Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?”
24 Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”
Da ya ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jama'a hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da Yahudanci.
Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!
Shi kuwa ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da 'yan'uwa waɗannan abubuwa.” Sa'an nan ya tashi ya tafi wani wuri.
Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse.
Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana.
Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.
Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?”