Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.
“Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan.
Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.
Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.”
Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.