Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.
Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.
Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.
Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”
Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa, “Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma,
Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.
Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”
Ka ɗauke ni mana, mu gudu, Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka. Da yake kana nan za mu yi farin ciki, Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki. Ya dace a ƙaunace ka!
Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo.
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.