Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe, Suna kawo mutanen Allah gida. Suna tafe da azurfa da zinariya, Domin su girmama sunan Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa.
Yanzu kuwa za ku kira al'ummai, baƙi, Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya, Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku! Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Zan sa dukan wannan ya faru, Zan ba ku girma da daraja.”
To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.
Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.