Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman?
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
Sai ya tashi ya tafi. Ga wani mutumin Habasha, wani bābā, mai babban matsayi a mulkin Kandakatu, sarauniyar Habasha, shi ne kuwa ma'ajinta, ya zo Urushalima ne yin sujada,
suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”
A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.
Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi.